����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MUHD*
No. 2⃣0⃣
Nan ya sauko yana tafe yana nemanta, sai dai sam bai ganta ba, gangarawa yai yaje Office d'in Habib ya bude tare da kallan Sagir, Sagir na ganinshi ya mik'e tare da cewa shigo mana Jalal, nan Jalal ya karasa tare da mikamai hannu, suna gaisawa amma yana waige waige, Sagir ya kalleshi tare da zare hannunshi yace " Jalal me kake nema?"
Kallansa yai yace " Na'am? Kawai nazo mu gaisa ne."
Nagode kwarai, abin ya ban mamaki baka tab'a ko zuwa inda nake ba sai dai ni na nemeka amma yau da kanka? Sagir ya fad'a tare da zama, Jalal yajuya yace bari na wuce ai mun gaisa, ya fad'a yana kallan office d'in Habib.
Sagir yace nagode Jalal, har yakai kofa ya juyo yace" Chairman shi kad'aine a office?"
Da mamaki Sagir ya kalleshi yace shikad'aine zaka shiga ku gaisa ne? Da sauri yace no, na tambaya ne kawai.
Yana gama fad'ar haka yai waje.
Jalal na rufo kofar yai ajiyar zuciya yace ina taje? Nan ya cigaba da nemanta gajiya yai da yawo ya samu wata kujera ya zauna yana d'an maida numfashi, ya d'an dade kafin ya koma inda suka saba zama, yana bud'e kofar ya karasa jiki a sanyeye zuwa inda take zama, sai dai abin mamaki jiyai ance " Deen ka dawo?"
Da mamaki ya kalleta idanunwansa cike da tambayoyi karasa wa yai inda take tsaye ta jingina da bango tana kallansa, kusa da ita yaje ya saki ajiyar zuciya yace " ina kika je? Kinsan neman da namiki kuwa?"
Wani sansanyar murmushin kauna ta saki sannan tace " naji dad'i daka nemeni."
Had'e rai yai sannan ya lankwaso babban yatsansa dana kusa dashi ya d'ana mata a goshi da sauri tasa hannu agun ta kalleshi kamar zatai kuka cikin shagwab'a tace me kuma nai?
Hararar wasa ya mata sannan yace " tambaya kike? Ina kika je? Kika sani nemanki?"
Gun takara sosawa sannan ta matsa daga jikin bangon tace suprise!!!
Kallan gun data matsa yai kwali ne mai fad'i a jiki akwai hoton pizza sai kuma ledar da yana hango lemon kwallin dake ciki, kallanta yai yace " nameye?"
Kai ta girgiza sannan ta zauna ta mai alama da hannu ya zauna nan ya zauna yana kallanta yace " menene?"
Hararsa tad'anyi tace "lunch zamuyi kafin in tafi." Murmushi ya saki sannan yace " abinda kika sauka yi kenan?"
Tace " eh so nake muci abinci tare." Kallanta yai sannan yace next time in zamuci abinci nizan siya banaso kid'ingayin abinda namiji ya kamata yai."
Aranta tace ina gani ba hali gareka ba yaza'ai in d'inga d'aurama wahala.
Sai alokacin ta tuna meya ce mata yanzu.
Ido tad'an rufe sannan tace " next time in zamuci? Kana nufin ba wannan bane last kenan? "
Ehem gyaran murya yai bai magana ba, Had'e rai tai tare da bud'e pizza sannan ta gutsira ta mik'amai sannan nan ya ansa suka fara ci, ta kalleshi tace Deen what are we?
Kallanta yai shima jikinsa yai sanyi cikin sanyin murya yace "we? Kodayake I think munzama we?"
Jiyai tace me kake cewa? Tafad'a tare da bud'e mai lemon ta mik'amai ya ansa tare da kallanta mantawa tai taci abinci da hannun kawai ta rufe idannunta, yaji ne ya shigar mata ido ta saki wani kara, tare da kokarin goge idannun da sauri Jalal ya rik'e hannun da take kokarin kaiwa sannan yai saurin kurbar ruwa ya kuskure bakinsa sannan ya matso a hankali ya fara hura mata idan da yajin ya tab'a, batasan sanda ta ware idanun ba, sam jitai yajin ya tafi kallansa take idannu a bud'e zuciyarta kuwa sai bugawa take da karfin gaske, karkatar da kai yai sannan yagyara zamansa, yace " u are soo clumsy taya zaki......."
Ganin yanda take kallanshi yasa ya hura mata ido yace Kallanfa? Da sauri ta mik'e tsaye d'an jitake kamar bazata iya numfashi ba ta mik'e tana bubuga kirjinta, da sauri Jalal shima ya mik'e yaje gabanta ya kalleta tare da cewa menene kikeyi hakan? Idanunta ta zaro tana kallanshi sannan ta runtse idonta tad'anyi baya daga inda yake, da mamaki ya kalleta yace " Mekike hakan?"
Juyawa tai sannan ta zauna agunta nad'azu tace " kawai nidai kad'an dingayin nesa dani."
Kallanta yai da mamaki yace " Bangane ba? Bakyaso inzo kusa dake? Ko me kike nufi?"
Seemah a hankali ta d'ago ta kalleshi tace " bafa haka nake nufi ba."
Fuskarsa ya matso kusa da tata ya shiga jujuya kai itakam jitai numfashinta ya d'auke, idanuwansa kawai take kallo? Yad'an daga sannan yace " kince bakyason inzo kusa dake amma idanunki sun nuna kinaso me kenan?"
A hankali tai ta furzar da iska tana cewa "Cool Down Seemah." Kallanta yai sannan ya d'au pizza ya kara ci, sai da ya gama ya matso kusa da ita tare da kamo kafarta ya ciro plaster d'in daya siyo ya sa mata a gun dataji ciwon nan, itakam kallanshi kawai takeyi, d'agowa yai yace ba fita zakuyi ba? Kallansa tai tace karfe nawa? Agoggon hannunsa ya duba yace 1 nima tashi zanyi inje mosque, nan ya mike tare da gutsirar katuwar pizza ya tura mata a baki yace " ba kallo ba kice abinci kije kar yayanki yai ta jiranki."
Ya juya ya fara tafiya, sai dayai d'an nisa ya juyo yace kuma ki kunna wayarki.
Ya juya ya fita, kallo ta bishi da shi jitai shakuwa ta zo mata, cire abinda yasa mata a baki tare da kara wata shakuwa, juice d'in ta d'auka tasha sannan ta baza tagumi tace " Seemah ya zakiyi? Haka ake soyayya ko kuma nawa ne hakan?"
Sama ta kalla hasken rana yasa tai saurin yin kasa da kanta, tace dole inyi tambaya kila ko ciwon zuciya gareni ko wani abun.
Tagama cin abinci sannan ta sa ragowar a leda ta mik'e.
Habib bayan sunyi Sallah ya kira wayar Seemah a kashe nan ya tura Sagir yaje ya dubo office d'in ko tana can.
Yana shiga ya tadda ta idar da sallah itama yace " madam ana jiranki."
Nan ta mik'e tare da cewa to, nan ta fito.
Sun shiga mota, Habib ya kalli Seemah yace " Kanwata me kike tunani?" Juyowa tai tace " Yaya baka tunanin wani abun zai kara faruwa ko? Ina tsoron kar abinda yafaru agidansu Hajiya ya kara faruwa.
Kallanta yai jiki a sanyaye ya sa hannu akanta yace " karki damu Seemah insha Allah ba abinda zai faru." Tace ka fad'ama dad zamune? Yace a'a ai ba sai na fad'amai ba in zamu gaida 'yan uwa, tace to.
© *NWA*
��♀
Tnx a lot, yau ba Kice komai ba, ba ta'aliki ne ko amsa ma jaruman naki cikin littafin....
ReplyDeleteLol
ReplyDelete