Tuesday, 20 December 2016

JALALUDEEN 19

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*


   No. 1⃣9⃣

   Haka ta karasa Office d'in Habib fuskarta d'auke da murmushi, da sagir suka gaisa sannan ta karasa kofar Habib tai knocking, nan ya bada izini ta shiga da Sallama, a zaune ta ganshi yana duba abu a laptop ga takardu a kusa dashi, tana shigowa ta karasa kusa dashi ta baya ta zuro kanta jikin screen d'in tace " Yaya baka ga kanwarka bane?"

  Juyo wa yai tare da zare medical glass d'inshi yace " Seemah kin iso?" Ta mik'e tare da hard'e hannuwanta tace " da alama bakaji dad'in ganina ba."

  Hannunta ya jawo sannan ya juyo yana kallanta yace " Sorry Kanwata wasu takardu ne zan tura Company d'in Dad na England."
  Kallansa tai ta turo baki cikin shagwab'a tace na hakura tunda dad d'ina zaka turama, yace yauwa zauna ki jirani na gama, amma fa sai munyi azahar zamu? Tace nasani yaya, ta fad'a tare da kallan agogon dake makale jikin bango, 11? Ashe zan d'ade?

  Mik'ewa tai tace "Yaya kai aiki a hankali ni bari inzaga inga Company d'in, yace to Seemah amma ki kula fa, tace ok.

  Fitowa tai direct tai hanyar gun aikin Jalal itakam bata ganin wani abun ne in taje gunsa, d'an su acan England mace d'an taje gun namiji ko ba saurayinta bane ba wani abun bane, Office d'insu ta isa ta murd'a tare da Sallama, juyowa sukai suka kalleta, karasowa tai cikin halin ko in kula tace " zaga yawa nake nazo kusa danan shine nace bari inshigo ku gaisa, kallanta sukai suka ce Shigo mana, Kallansu tai yanda taga suna za-zaune yasa ta game meeting suke, Jalal ta kalla, kallanta yake shima fuskarsa d'auke da murmushi,  shigowa tai ta karasa ta zauna daga gefensu, tace " karku damu dani kucigaba da aikinku."

  Nan suka juya suka cigaba da meeting d'insu sai dai jefi jefi suna kallan juna a sace itada Jalal, suna cikin meeting ne wata tai knocking tare da bud'e kofar ta shigo,  Seemah ta kalleta kana ganinta kasan Christian ce daga yanayin shigarta, siket ne iya gwiwa da riga coat sai da bata rufe mab'alin saman rigar ba hakan yasa inta sukunya zaka iya gano kirjinta.

  Cikin salo ta karaso tare da tsayawa kusa da Jalal, Seemah kam idanta na kanta, matar ta kalli Jalal tare da mik'amai takarda cikin kissa ta zubar da takardun Jalal ya sunkuya zai d'auko itama cikin salo ta sunkuya, tare da rike hannunsa tace " Barshi........." da karfi aka katseta tare da cewa " Let go of that hand."

   Da mamaki kowa ya juyo ya kalleta Jalal ya fizge hannunsa tare da makama matar harara yace " what are you doing?" D'agowa tai ta kalli Jalal sannan ta kalli Seemah tace " Who is She?"

Karasowa Seemah tai tace " what? Baki da da'a ne? Ko dama tambada ne ya kawoki nan?"

  Matar ta kalleta tace " meye damuwarki a ciki?" Yanda tai maganar zakasan hausan bata gama zama mata ba.

  Harararta Seemah tai tace " meye nawa kuwa a ciki? Sai dai bazan bari ina kallo mace irinki ta nemi lala......"

  Jalal ne ya katseta yace " ya isa haka, abar maganar haka."

  Seemah cikin takaicin da batasan kanshi ba ta kalleshi sannan tai waje da sauri, Jalal ya bita da kallo sannan yacema matar ta fita, abokanan aikinsa suka kalleshi sukace ina taje?

Ido ya runtse sannan yace ina zuwa yai waje da sauri,  dubata yafarayi tundaga office d'insu sai dak bai ganta ba, tunanin gun da suke zama ne ya fad'omai dasauri ya karasa gun elevator ya tab'a sai dai abin haushi tana kasa hakan yasa kawai ya wuce beni yafara hawa da sauri, matatakalar nada yawa sosai amma sam bai kula ba yana isa yai saurin karasawa kofar ya bud'e, tare da duba inda take zama, a zaune ya ganta ta had'e kai da gwiwa tana kuka ita kanta batasan meke damunta ba sai dai abu d'aya daya bata haushi katseta da Jalal yai tana magana, Jalal ya karaso gabanta ya tsugun na, cikin sanyin murya yace " me kike anan?"
  D'ago jajjayen idanunta tai ta kalleshi cike da mamaki yace kuka? Meya saki kuka?

  Harara ta makamai sannan tasa hannu ta share hawayenta jiyai zuciyarsa ba dad'i yace " Haushi kikaji? D'an ta rik'eni?"
  Cikin masifa tace " Yama za'ai ka d'inga bari mata na tab'aka?"

  Yace " kin kula kuwa? Bafa da saninta bane."
Cikin abin kuka tace " kare mata zakai? Bayan ina ganinta? Tashi ka bani guri tunda kare mata zakai, daga yanzu kuma bazan kara damuwa ba in wata ta tab'aka."

   Murmushi yai yace " Don't tell You are jealous? "
  Da sauri tace " ni? Inji wa? Akan me zanyi kishin?"
Ya kara sakin murmushi sannan yace " haka ne bayan na san kin tsaneni."
  Nan ma da sauri ta kalleshi tace " nidin? Injiwa? Waya fad'ama na tsaneka?"

  Kasa yai dakai yana murmushi idanunsa ne suka kai kan kafarta da alama takalmin yajima dunduniyarta ciwo garin sauri ko gudu datai d'azu, hannu yasa ya zare mata takalmin kafarta, kallansa tai cike da mamaki tace " menene?"
  D'agowa yai tare da had'e rai yace " gudu kike d'azu?"

  Kai tad'aga tare da kallan sa, iska ya d'an furzar yace " in zaki d'inga gudu kidaina sa irin takalmin nan gashi kinjima kanki ciwo."

  Murmushi ta saki sannan tai kasa dakai ahankali tace "are u worried about me? "

  D'agowa yai ya kalleta nan suka kurama juna ido a hankali ta lumshe ido, Jalal ya kura mata ido shikam bai tab'ajin abinda yakeji a wannan lokacin yana tsirgamai ba, itama idanun data lumshe jitake kamar me, wani irin so ne ke tsirga mata.

   Ajiyar zuciyar da Jalal yai ne yasa ta bud'e ido ta kalleshi yace " nabar wayata a office nasan za'a nemeni bari naje mu karasa, ko zakizo mu koma?"

  Tace " inafa zan koma bayan na gamajin kunya." Murmushi yai sannan yace " karkisa takalminki ki bari sai na dawo zan taho da plaster."

  Kai ta d'agamai nan ya juya yai gaba.

  Kallo ta bishi da shi basai ta tambaya ba soyayya ce ke yawo da ita, yau ta tabbatar da hakan dan ita kad'ai tasan metaji da taga mace tana neman jan ra'ayin Jalal, ajiyar zuciya tai tace " My First Love?" Da sauri ta rufe fuskarta da hannayenta alamar kunyar kanta take.


  Jalal na komawa suka shiga tsokanarsa meye tsakaninsu, had'e fuska yai yace " meye tsakaninmu kuwa? Kufa kun iya gulma bana kuma san haka, aiki mukeyi muyi mu rabu banasan a d'inga sako personal matters aciki." Jin haka yasa sukai shiru nan suka cigaba.

Basu wani dade ba suka gama, da sauri Jalal yai waje..........

  Da sauri ya fita yaje ya siyo plaster ya koma ciki, saidai yana zuwa cikin zumud'i ya bud'e kofar tare da shiga,  sai dai abin daya bashi mamaki ba Seemah ba alamarta nan ya shiga duba gun sam batanan kansa ya shafa tare da cewa ina taje? Waya ya d'aga ya k'irata sai dai wayar a kashe take, juyawa yai ya fito.






© *NWA*



��‍♀

©

No comments:

Post a Comment