Saturday, 17 December 2016

JALALUDEEN 17

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*


   No. 1⃣7⃣

  Farida na fita itama ta kashe wayarta ta zuge jakarta tasata tare da kara kwanciya, Ammar takesan k'ira sai dai bazata kunna wayarta ba, daga bayama mik'ewa tai ta dawo falo ta zauna gun su Ra'is, ganin ansa wani indian series *JODHA AKBAR* a tv yasa tafara kallo, sai dai abin haushi tamaji gaba d'aya yawancin maganar dazasuyi sai sunce _Jalal_ jitake kamar da da ita suke haushi ya kamata ta canza tasha, Farida da Aisha dakw zaune suna kallo sukace Seemah lafiya? Aisha tace"Dramar fa tanada kyau sosai banaso ko kad'an a wuceni."

  Haushi ya kama Seemah tace " meye wani Jalal in suna san abin ya birge mutane sai su nemo suna mai dad'i ba wannan ba."

  Cike da mamaki farida tace " meye da sunan? Nikam ina san sunan har tunani nake in na k'ara haifar namiji a samai.......
Seemah ta mike tare da katseta tace " mene? Aunty badai wannan sunan ba gaskiya." tana kai nan ta juya tai ciki, Aisha ta bita da harara tace wlh Aunty wannan da kanwatace zaneta zan d'ingayi sam ta raina mutane.

  Farida tace ya isa haka ni kaina abinda takeyi ba dad'insa nakeji ba amma akanta zan iyacemiki Habib zai iya rabuwa dani, d'an tun kafin muyi aure yakemin zancenta sannan sanda za'a kawo kud'i harda wani cewa zai nuna mata hotona ya tabbatar tana sona." Tai ajiyar zuciya tace " Bakisan abubuwan da akamin na takaici akanta ba daga baya dana gane san da suke mata ne yai yawa yasa nima nafara cusa kaina gunta kankice me tafara sona ko kunya Habib kecemin yaji dad'i da Seemah take sona nima nake santa d'an bazai iya zama da wacce batasan kanwar sa ba."

Ta kalli Aisha data saki baki tanajin zancen tab'e baki tai tace " tab lalai kice inyi a hankali mu rabu lafiya."
   Farida tabi inda Seemah tai da kallo tace " Gaskiya kam."

  Seemah kam d'aki ta shiga ta zauna a bakin gado tare da turo baki gaba masifar da Jalal yamata dazu, kwafa tai tace amma nima banza ce kuma dayamin masifar banajin nafad'amai abinda zai dameshi....

♡♡♡♡♡♡♡♡♡



   Dad sam yakasa tsaye bare zaune abin duniya ya dameshi, ya zaiyi ya birne kar a kara tada maganar da akasha gwagwar maya a baya d'an binne ta? Tsoronshi d'aya kar lokacin da Seemah zatazo ace za'a aurar da ita magana ta tashi, ya zaiyi shikam, bayaso sam ran Seemah ya b'aci bare har taji wannan labarin da zai ruguza farin cikin rayuwarta, iska ya furzar sannan ya zauna a gefen gado tare da rik'e kansa, ya rasa ina zai fara jawo mafita.

   Matarsa ce tashigo tare da zama kusa dashi hannu tasa da dafashi cikin salon jan hankali tace " Dad d'in Seemah me ke damunka ne? Wani ne ya b'ata maka rai?"

   Hannunta ya ture daga jikinsa yace" dan Allah fita ina inasan nakasance ni kad'ai."
   Kallansa tai tare da manna mai kiss na kissa a kunci, mik'ewa yai cikin b'acin rai yace in bazaki fita ba ni bari na bamiki d'akin.
  Yana kai nan yai waje tabishi da harara tace " wlh badan kud'inka ba banga dalilin dazai zaunar dani kanamin abinda kaga dama ba.

   Dad kam falo ya fito anan yaga Junaid da Ammar suna hira, zama yai tare da cewa Ammar kunyi waya da Seemah kuwa? Nak'ira wayarta d'azu a rufe, Ammar yai ajiyar zuciya yace " Dad nikaina bansan meke damun kanwata ba, a iya sanina bata tab'a kashe wayarta sai dai in ba charge sannan kullum mukai waya sai inji kamar tana cikin damuwa."

   Junaid yasa dariya yace " kaii Ammar gaskiya ina tausayama wanda zai auri Seemah d'an na kula dakai da Dad bazaku barsu ba, kuna jin ranta ya b'aci zaku bazama zuwa gidan."

   Dad ya harareshi yace " dama kai na kula baka san kanwarka sosai shiyasa baka damu da ita ba."

  Junaid yace " wlh Dad ina bala'in san Seemah banaji in wani abu ya sameta zan iya rayuwa, ai Dad tun tana jaririya kariga ka cusa mana santa shiyasa kowa ke kishin gata da so da muke mata."

   Ido Dad ya lumshe yace " yanzu misali in wani abu ya sameta na tsanani zaku gujeta?"

  Da sauri Ammar yace " Haba Dad ai bana tunanin akwai abinda zai sameta muna raye in kuma Allah yatsara hakan zai faru kaima kasan soyayyar da muke mata bazatasa mu gujeta ba sai dai muzame mata makafa."

  Junaid ma yace " Dad adaina maganar nan."

Nan suka d'auko hirar abin dariyar Seemah datana yarinya.....

  Dad kam hankalinshi duk baya kan hirar sosai.


□□□□□□□□□□□□□□□□□□□



Jalal bayan sunyi Sallar Magrib ya fito waje d'an d'akin nasu ba dadin zama su hudu ne a d'aki kwaya d'aya tun safe in ya fito basan komawa yake ba saj bacci, zama yai a wajen kantin wani abokinsa wayarsa ce a hannunsa yanata juyata, abinda yama Seemah d'azu ne ya fad'omai yace " did I go too far?" Kansa ya sosa yace nasan halinta ba wani haushi zataji ba, kafin gobe zatamin text ko bata k'irani ba.
   Mai shagon ne ya kalleshi yace " Jalal tunanin me kakeyi haka? Ko dai ka fad'a ne?"

"Ina na fad'a kuma?"
Dariya mai shagon yai yace " kai Jalal gaskiya kaima sai a slow, nifa ban tab'aji kace ga budurwarka ba, duk matan dake sanka, ka manta matar nan mai mota....."

   " naji ya isheni karma ka tado min da wannan bakin cikin"

  "Amma Jalal matar nan kamar fa zata haifeka,"

  Kai Jalal ya girgiza yace " ni dai d'an Allah kabarni, yauwa dan Allah Nafi'u ga tambaya, nasan ka namamajo ne kai, inajin 'yan matanka sun kai 5, d'an Allah ya keke gane mace na sanka."

  Dariya sosai Nafi'u yai yace " lalai Jalal abin naka babba ne amma kafin ka nemi sanin ana sanka ai kanka zaka fara tambaya, kanasan wace kake so........"

   D'aga mai hannu yai tare da mik'ewa yace kai fa matsalata dakai kenan, ce maka nai ni nakesan ji ko me? da zaka faramin zancen banza nifa banaji akwai wani guri a zuciyata na soyayya, aiki na shine a gabana burina inga......."
  Sai kuma yai shiru tare da cewa na tafi, yana kainan ya wuce ya fara tafiya.

  Nafi'u ya bishi da kallo yace " Jalal kenan ko baka fad'aba na kula kafara fad'awa san wata, d'an tunda nake dakai yauce rana ta farko daka fara tambayata akan soyayya.



  Jalal yana shiga d'akinsu yaga ba kowa, tunani yai bari ya d'auko takardun dasuke aiki a kai ya duba kafin su dawo su cikashi da magana, sai dai me? Kaf ya duba inda yake ajiya ya rasa cike da mamaki yake tambayar kansa to ina nasa? Nasan dai tabbas na fito dasu daga office har nabiya gun Assistant Director na nuna mai nakuma fito dashi, to ina nakai?

  Kansa yad'an buga kad'an yace " motar Seemah? Oh Gosh" gashi dole gobe zasuyi amfani da takardun da sauri ya d'au waya ya k'ira ta sai dai abin haushi wai a rufe, text ya mata akan inta bud'e waya ta kirashi sai dai shima bai yi delivery ba, yama rasa ya zaiyi, lalai dole gobe kafin ya tafi gun aiki ya biya ya anso.


   © *NWA*


��‍♀

1 comment: