Thursday, 29 December 2016

JALALUDEEN 29

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*


*_This page is dedicated to you My Intimate Friend Aisha Muhd Umar, May almighty Allah grant all your good wishes_* ........



   No. 2⃣9⃣

   Jalal haka ya zauna yaci abincin nan bayan ya gama ne ya kalli Zainab dake gogema Zahee jiki yace " Umma fa?" Tace tana d'akina, ya mik'e tare da cewa bari in ganta tace to, har yakai bakin kofa a hankali yaji tace " Yaya?" Jalal ya tsaya ba tare da ya juyo ba, tace " nasan akan me ranka ya b'aci saboda Abba yaje aiki ne, sai dai kayi hakuri yaya amma Abba saboda harkar auranmu yake tara kud'i" da sauri Jalal ya juyo ya kalleta tai saurin yin kasa dakai tace " tun bayan ankai kud'i Abba kullum sai ya fita yin aiki, duk dabansan wasu aiyukan yakeyi ba amma naji dakansa ya fad'i dalilin aikin da Umma ta tambayeshi."

  Jalal jiyai kamar an kwaramai ruwan sanyi, cikin sanyin jiki ya zuge labulan ya fita, ya na fita ya tsaya a jikin bango ya zaiyi? Shidai gaskiya magana d'aya ba yazan Zainab, a matsayin kanwa ya d'auketa ba wai a soyayyar aure ba, yai shiru can ya taka zuwa d'akin Zainab, bayan yayi Sallama Umma ta amsa daga ciki ya zuge labulan d'akin a bakin kofa ya tsaya, ko ba komai yasan Zainab akwai tsafta da san gyara, kallan Umma yai cikin sanyin jiki yace " Umma inada magana." Ta d'ago ta kalleshi, sannan tace ka zauna sai muyi maganar, a kasan ledar d'akin ya zauna sannan yace " Naso sai Abba ya dawo in fad'a muku gaba d'aya amma yanzu sai nai tunanin gwara ma fara sanar dake."

  Ta kalleshi cikin damuwa tace " menene Jalal? Wani abun ne ya faru?"

Kai ya jijiga mata yace "ko d'aya kawai dai inasan insanar daku abinda ke rainane."

  Umma batai maganaba amma ta tattara hankalinta gaba d'aya kansa, Jalal yai kasa dakai yace " a gaskiya Umma inada wacce nakeso, ina santa sosai kamar raina, sannan banaji zan iya auran wata ba ita ba.."

  Gaban Umma ne ya yanke ya fad'i cikin tsananin firgice da tsoron kalaman Jalal tace " Jalal me kake nufi da kalamanka?"

  D'agowa yai ya kalleta yace " Umma kinsani sosai tunda ke kika haifeni, kinfi kowa sanin Zainab a matsayin kanwa ma d'auketa kamar yanda Zahee take a guna."

   Umma ta mik'e taye ta matso kusa dashi ta rik'e hannayensa cikin rud'ani tace " Jalal dan Allah karkabar mahaifinka yaji wannan zancen, d'an inyaji daga ni har kai bansan abinda zai mana ba."

  Jalal ya runtse idanunsa yace " Umma please ku barni ko sau d'aya nai abinda nakeso, tun dana taso bam tab'a yima Abba musu ba arayuwata, hatta abinda zan karanta a jami'a shiya zab'amin da kansa ba wai san raina bane, d'an Allah Umma wannan karan ya shafi rayuwata gaba d'aya ki taimakamin......"

   Idanunta suka ciciko ita kad'ai tasan wahalar da d'anta ya sha, to amma ya zasuyi? Ko ita tanasan Zainab.

   Zatai magana aka yaye labulan da karfi akace me kace Jalal? Juyawa Umma tai da sauri ta kalli Abba da idanunsa suka kad'a sukai jaa na b'acin rai, Jalal yai kasa dakai yace " Abba ina kwana?" Ran Abba yakara b'aci yace nace me kace? Ya fad'a tare da shigowa ciki, Jalal ya d'ago a hankali yace " Abba inada wacce......."

Cikin tsawa Abba yace " kada ka kuskura ka kara maimaita kalaman nan,  kafi kowa sanin Zainab itace matarka ko kaki koka so."

  Jalal ya d'ago ido ya kalli Abba, shikansa yasan yauce rana ta farko daya tab'a musanta maganar mahaifin nasa yace " Abba dan Allah ka barni na auri wacce nake so,  wlh yarinyar nan itama ba ruwanta."

  Abba ya fusata yace " yau ni Jalal zaka kalla ido cikin ido kacemim wai in barka ka auri wacce kake so? Anya kuwa kaine Jalal?"

  Kasa kawai Jalal yai da ido jiyake zuciyarsa na tafasa, Abba cikin takaici ya bar d'akin yai waje da sauri, Umma ta kalli Jalal cikin tausayi sai dai batasan me zatace ba itama ta fito, Zainab data fito daga d'akin Zahee jin hayaniya ta kalli Umma tace " Umma lafiya?" Umma takasa amsa mata kawai d'aki ta wuce.

  Jalal kam jin zuciyarsa na zafi kawai yai saurin kiran Seemah, tana zaune kusa da Ammar tana ganin kiransa ta kalli Ammar tace "yaya saurayina ya kirani." Da mamaki ya kalleta sai dai kafin yai magana ta gudu d'aki, tana shiga ta d'aga tare da sakin ajiyar zuciya, jin shiru yasa tace Deen? Kanaji na?

  Wani abu ya had'iya sannan yace " Meemah ya kika tashi?"

  Ta kwanta akan gado tare da jan bargo tace " na tashi lafiya sai missing d'inka dake neman yimin yawa."

  Bai san sanda ya saki murmushi ba yace " Na isa fa?"

  Da sauri ta yaye bargon tace " da wuri haka? Hmm kunyi maganar? Sun yarda? Ya kukai?"

  Dariya yasa sosai yace " duk ni kad'ai? Wanne akeso in amsa?"

  Dasauri tace" ya kukai please? Fad'amin kaji?"

  Murmushi yai yace bamuyi maganarba tukun yanzu na iso, tai ajiyar zuciya tace " ahhh jinai kamar zuciyata zata fito dan tsoro."

  Ya kara sakin murmushi yace" da ina kusa dana ba ki......" da sauri ta sa hannu a goshinta tace " wayyo zafi" tai maganar cikin shagwab'a, dariya ya saki tace " Deen me na maka ka d'ana min?"

  Dariya sosai ya d'ingayi yace " Ahhhh that's My Meemah you always make me laugh."

  Tai murmushi tace " In mukai aure sau 10 zan saka dariya a rana."

  Dariya ya sakeyi zai magana yaga Zainab a tsaye a bakin kofa idanunta sai zubar da hawaye sukeyi,  kallanta yai sai yace ma Seemah" zan kiraki anjima." Tace okay miss u...... katse layin yai ya kalli Zainab, ya mik'e zai zo gunta da sauri ta juya da gudu tai waje , kai ya dafa yace " Ya Allah gani gareka."

  Seemah kam kwanciya tai ta rungume pillow a kirjinta tace I miss you Deen Muah......sai kuma tai saurin liliba da bargo wai ita a dole kunya jitake in aka rabata da Jalal to lalai  karshen rayuwarta yazo.

  Mikewa tai ta sauka kasa ta zauna kusa da Ammar, kallanta yai yace " kingama waya da saurayin?"

  Ta rufe idanta da hannu biyu sannan ta bud'e ido ta kama hannunsa tace " Ya Ammar ina tsananin san Deen, jinake in aka rabani dashi kamar........"

  Had'a rai Ammar yai yace " bana ce karki kuskura kiyi irin wannan soyayyar ba?"

  Ta kalleshi tace " ni kaina Yaya bansan ya akai nazama haka ba."

  Ya mik'e tsaye yace da alama ma kinfi sanshi akaina, dariya ta saki tace kai yaya ka manta kai Special Oppa ne?
  Ya harareta baice komai ba, ta taso ta rike hannunsa tace " yaya bansan meyasa Dad bayasan Jalal ba."

  Da mamaki Ammar ya kalleta yace " ya ganshi ne?" Tace " a'a kawai daga fad'amai inada wanda nakeso naga ransa ya b'aci."

  Ammar yai murmushi yace" that means ba saurayin naki bane baiso, bayasan kiso wani ne."

  Tai shiru can tace kuma fa hakane to meyasa? Ya ce inazan sani? K'ila bayasan ki raba hankalinki ne, kina karatu ga soyayya.

  Ta jinjina kai Ooooops Nagane maganar.






© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

  ��‍♀

No comments:

Post a Comment