Wednesday, 14 December 2016

JALALUDEEN 12

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MOHD*


   No. 1⃣2⃣

  Habib kam sam jiyai gidan ya isheshi hakan yasa yace zasu wuce, sun musu sallama sannan suka fito, harsun zauna a mota yaga yanda idan Seemah ya kad'a yai jaa kawai ya bud'e motar ya koma ciki, suna zaune sunyi tagume sallamar Habib ne ya katsesu, da sauri suka mik'e suka fito.

    Habib yace " har na shiga mota naga kamar ya kamata inji menene dalilinku na k'in sakema Seemah?ko d'an bata tab'a zuwa ba sai yau?"
   Kawo yai saurin cewa shine dalili yaza'ayi ace sai yau zata tab'a zuwa gaidamu?
  Kallansa Habib yai bayajin zuciyarsa ta gamsu da maganar saidai tunda sunce hakan yace " ayya amma kawo kasan ba laifinta bane Dad ne yake hanata zuwa."

   Hajiya tace to jeka ku tafi ko ka manta kanada aiki ne?
  Nan Habib ya juyo ya shiga mota, dad'insa d'aya yana shiga yaganta tana waya da Ammar sai dariya take, hakan yasashi dariya, sun fara tafiya shima yanata janta da hira, bayan sun shiga Abuja ne ta kalleshi tace "yaya muje Company sai anjima sai in koma gida."
  Yace "shikenan dama yau driver d'inki zaizo sai yazo ya d'aukeki"

  Murmushi tasaki a ranta tace Jal we will meet again.

Suna isa Company d'in Sagir yazo ya sanar ma habib akwai meeting dazasuyi yanzu, nan ya kalli Seemah yace kije office d'ina tace to nan ya juya a hankali tace Sagir? Juyowa yai yazo kusa da ita, tace " ina Abokink?"
  Cike da mamaki ya kalleta? Yace wa kenan?
kallansa tai batare datace komai ba hakan yasa yace Jalal? Ta had'e rai tace " yana ina?  D'an yau sai na zabgamai rashin mutunci.

  Kai ya jinjina yace hmm yana office a k'irashi ne?, tad'an juya kai tace inane office d'in ku ba meeting zaku shiga ba? Nuna min kawai.

   Yace a third floor yake kina shiga daga hagu zakiga Department d'insu, tace ok ta juya tai gaba, Sagir yace " Yau kuma wani fad'an za'ayi?"
  
  Elevator ta hau ganin ba kowa yasa tad'an fito da madubi daga jakarta tad'an duba fuskarta murmushi tai sannan tad'an sa janbaki kad'an tace " yau sai ka kasa ganeni."
   Tana isa tai inda akace tare da murd'a kofar tai sallama, office ne babba sai  dai kowa da desk d'inshi sai gurin da aka kewaye ma manager, sunajin sallamar suka juyo gaba d'aya suka zuba mata ido, kallansu ta shiga yi sai dai bataga Jalal ba, karasawa tai ciki tace " Jalal nake nema?" Wani ya matso kusa da ita yace ga desk d'inshi nan ya fita inaji ko kasa yaje submitting d'in proposal.

   Desk d'in ta kalla sannan tace bari na jirashi, karasawa tai ta zauna a inda yake zama tare da bud'e takardun dake gun, kowa sai kallanta yakeyi, manager d'inne ya fito ganin Seemah yasa ya karasa da sauri yace " Ranki ya dad'e me kikeso? Ai da baki zo ba kin turo kawai."

  Had'e rai tai tace " inasan ganin Jalal ne d'an yau banajin zan iya kyaleshi."
Yawo ya had'iya aransa yace Jalal me kayi?
  A fili yace " ayi hakuri Madam......."
Katseshi tai tace " asa a k'irashi yanzun nan."
Nan ya fita da sauri yai waje, Seemah ta kalli ragowar tace " kucigaba da aikinku." Wata mace ce tad'an matso kusa da ita tace " laifin me ya mik'i? Naji dad'i da kikace zaki hukuntashi dama haushi yake bani, farkon zuwa na ina bala'in san mutumin nan har abinci nake zama a gida in had'omai sai dai duk wannan wahalar danake bazai ci abincin ba kuma baya kulani, rannan ma ba ka ra yacemin bayasona."

   Seemah ta saki dariya tace " ke meya kaiki san wanda baya sanki? Ai kece mak kuskuren ba wani ba."
Haushi ya kama matar ta juya ta zauna a ranta tace " Allah yasa kema kiyayyace ba so kike masa ba."

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

  Jalal ne ya shigo da sauri yana neman me nansa, kallan kowa ya shiga yi yaga suna nunamai desk d'insa karasawa yai desk d'in d'an baya gano kowaye tunda ta juya kujerar baya tana game, jin sallamar Jalal yasa ta kashe game d'in tana jiran k'arasowarsa.
  Jala mamaki yake wani rik'eken ne wannan? yana zuwa gun yace " excuse me"

   Seemah ta juyo da kujerar ta cik'e da mamaki ya kalleta yace " You?" Gira yad'agamai sannan ta mik'e tare da had'e rai tace " Follow me."
  Tana kainan tai waje, hartaje kofa taga bashi da niyyar tahowa haushi ya kamata ta juyo tazo inda yake cikin magana mai rad'a tace " so kake in jaka da kaina?"
  Yace muje.

Sun fito ta kalleshi tace " kar mutane suganmu ka sameni a gun jiya rooftop,  tana kainan ta wuce.

  Iska ya furzar yace " Ahh wannan tagama rainani, me? In sameki a ina?" Sai a lokacin ma yabi bayanta da kallo, atamfa? Shi da sam bai kula bama, daga kanta yafara kallanta har kan takalmin datasa mai tsini sosai, tayi kyau sosai, wani b'angare na zuciyarsa ya fad'a da sauri ya girgiza kai sannan ya wuce shima.

   Ta rigashi isa hakan yasa ta karasan can bango tana kallan kasan titi yanda motoci suke wucewa, Jalal ne ya bud'e kofar tare da kallan inda take tsaye murmushi yai sannan ya karasa gun, gefenta kad'an yaje ya tsaya, batare da ta kalleshi ba tace " a haka mutum sai yaga kamar kowa na duniya yana cikin kwanciyar hankali."

   Kallanta yai sannan ya kalli kasa yace " a binda mutum yake gani daga nesa dama haka yake ai sai kiga kamar kowa yana walwala, amma me ya kawo ki office d'inmu?" 
 

  Juyowa tai ta kalleshi sannan tace " ya kagan ni?"

  Kallanta yai kad'an sannan yad'auke kai yace " bangane yaran ba?"
  Leb'enta tad'an ciza sannan tace " kalleni da kyau ka gani baka ga komai ba?"
   " Banga komai ba, akwai abinda yakamata in gani ne?" Ya fad'a yana kallanta.
Haushi ya kamata ta juya cikin fishi zata wuce tsinin takalminta ne ya shige d'an rami tai wala wala zata fad'i da sauri yasa hannu ya tarbota kallan juna suka fara, Seemah kam zuciyarya sai duka take, kallanta yai sannan yace " da saninki ko? So kike in tare ki."
  Harararshi tai tace " nina saka?" Baya yai da ita kamar zai saketa, kara tad'an saki yace " au ashe kina tsoro."
  Cikin shagwab'a tace " da yarda ni zakai?"
  Kai ya rangwab'ar yace " sai in yadda ke indai baki fad'amin me zan gani ba."

  Hannu tasa ta rufe idanta a hankali tace bakaga kayan danasa ba?

  D'agota yai ta tsaya daidai sannan ya juya ya kalli titi yace " au sai yanzu na kula ai."

   Haushi ya kamata tace " hakama zakace?"

  " a ina kika ari kaya? D'an a yadda kika nuna baki da wani kayan hausawa sannan jiya kika siyo naki nasan a k'ala baza........"

   Zuciya ta kawo mata wuya jakarta ta d'aga ta kwad'a mai a kafa, tace " kace ka gani ko yamin kyau shine bazaka iya ba? Gwara ka cimin mutunci?"

   Juyowa yai yace zan iya tafiya?
Haushi yakara kamata tace kabar kasar ma,

   Juyowa yai zai tafi sai dayaje kusada kofar fita ya juyo yace " kayan kasarmu sunfi miki kyau."
Yana kainan ya fita, kallan kofar tai sannan tai murmushi tace " kafad'i hakan tun d'azu shine bazaka iya ba?" Baki ta murgud'a sannan ta juya ta cigaba da kallan titi tana kallo tana murmushi. .....











© *NWA*

��‍♀

No comments:

Post a Comment