Sunday, 18 December 2016

JALLUDEEN 18

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*


   No. 1⃣8⃣


Da safe Jalal yana tashi ya shiga k'iran wayar Seemah sai dai a kashe ba shiri yai wanka ya fita gidansu ya wuce direct duk da bayasan Habib ya ganshi, yayi sa'a yana shiga layin motar Habib na fita daga unguwa karasawa yai tare da tambayar me gadi a k'iramai Seemah, kallanshi mai gadin yai sannan yace wani abun ne?

  Jalal yace ka k'irata mana sai ka gani.
Nan ya juya ciki, bayan ya kwankwasa Farida ta bud'e tare da tambayarshi menene? Yace wani ne ke neman Hajiya Seemah, mamaki ya kamata tace " Seemah dai?" Yace eh.
"Bacci takeyi kuma ba'a tashinta in tana bacci" ta fad'a tare da juyawa ciki.

  Mai gadin ya karaso ya fad'ama Jalal haushi ya kamashi, bacci?  Kuma ba'a tashinta?  Juyawa yai ya koma Company.

  Yayi sa'a sai 12 zasuyi meeting d'in hakan yasa ya zauna ya cigaba da aikinsa.

《《《《《《《《《《《《

  Seemah kam sai 10 ta tashi tai fad'a toilet tai wanka, Kaya ta gani a gefen gadonta guda 5 ta kalli kayan sannan ta fito daga ita sai towel tai falo, a dinning tagansu suna breakfast tace " Aunty kayan meye a side-bed d'ina?"
   " d'inkinkine jiya danaje nasamu ya gama wad'an nan"

   Tace ok nagode, ta fad'a tare da juyawa, ita meya dameta da d'inkin bayan Wanda tasai kayan dan shi ya shareta, muryar Farida ta jiyo tana cewa na manta Seemah yayanki yace inkin shirya kibishi office in ya fito sallar Azahar zai kaiki gidan Baffa(kanin dad) farin ciki ne ya bayyana a fuskarta ta juya tai ciki da sauri, ni kaina na kasa gane farin cikin me take, na zuwa gidan baffa ne, ko na zuwa company ko zataga Jalal?

  Atamfa tasa d'inki ya zauna mata sosai, ba wani kwalliya takema fuskarta ba tana gama da d'ankwali Aisha ta shigo tace kawo in d'aura miki, nan ta zauna Aisha ta d'aura mata ta kalli kanta a madubi tace " Aisha kin iya d'auri." Mayafi ta d'auko tasa sannan ta d'auko takalminta me bala'in tsini tasa, Aisha tace " Seemah bakya gajiya da tafiya da wannan takalmin?"

" ni in bashi nasa ba ban fiya jin dad'i ba" tafad'a tare da lank'aya jakarta ta fito.

  Bata wani ci abincin kirki ba ta fito.

  Suna fita kad'an Jalal ya kara zuwa mai gadi yace yanzun nan ta fita, cikin damuwa yace ina? Mai gadin ya kalleshi yace saurayi wai kai d'in waye?

Tunani yai maybe company d'in zata hakan yasa bai ba mai gad'in amsa ba ya juya yai gaba akan machine d'in daya kawoshi.

  Seemah motarta ta tsaya a Company d'in ta kalli Bala tace " bala d'an tsalaka can layin ka siyomin kati ta fad'a tare da mikamai 1000." Zuciya d'aya ya amsa tare da fita, ta kalleshi tace oh ko a ina nasan wani layi da ake sai da kati, u are the fool for believing me.

  Hoda ta d'auko ta shiga gyara fuskarta tad'auko jambaki pink zatad'an kara taji an kwankwasa mata glass daga gefen da take, a hankali ta d'ago tare da saurin maida kayan kwalliyar.

  Jalal ta fad'a a ranta, kallansa tafarayi shi kanshi kallanta yakeyi, can ya d'aure yace " meya sami wayarki?"

   Dad'ine ya ziyarci zuciyarta tad'an juya kai tace " ka k'ira ne?"

"Sosaima in fact tun jiya nake k'iranki"
murmushin farinciki ne ya kamata ta juyo tare da cewa " naga jiya da masifa muka rabu k'iran kuma nameye?"

  Cikin ba zatan kalmominshi taji yace " mantuwa nai a motarki"

  Kuramai ido tai cikin jin haushin kalaman tace " mantuwa?" Kai ya d'aga yace d'an mikomin takarduncan? Ya fad'a tare da nuna gefen gun da take da hannu, ita sai alokacin ma ta gansu haushi ya kamata ta janyo wani blank sheet dake kasan motar tace wannan? Jalal yace bashi ba, ta d'an juya kai alamar tana neman wani abun kwalin cassette tagani ta d'auko tareda cewa "oh wannan? Kai Jalal ya girgiza sannan ya zagaya d'ayan bangaren ya bud'e motar tare da tura kanshi itama ta turo kanta zata d'auka jisukai kansu ya gwaro kum! Kara tad'anyi tare da janye kanta ta rik'e gun shima d'an baya yai tare da kallanta, d'agowa tai zatai shagwab'a sai kuma ta kwashe da dariya ganin yanda yake kallanta, shima dariyar yasa harda zama a motar dariya sukai sosai, Sai da suka tsagaita Seemah tace " dama kana dariya haka?"

  D'an d'aure fuska yai yace " wato da saninki kenan kinsan takardun da nake nufi jan magana ne ko?"

  Murmushi ta saki tace " eh mana baka b'atamin rai da cewa wai ka k'irani bane kawai d'an takardu ba?"

  Kallan yanda take magana yake ta juyo tace menene? Yace Seemah nikam duk maganarki kamar shagwab'a kike kodai nikike ma haka?

   Harara ta makamai tace " kai kuma a me kenan?"

  Zuciyarsa taji ba dad'in kalmar sai dai daure wa yai ya d'au takardun yace shikenan.

  Da sauri tace " Deen"
  Juyowa yai ciki da mamaki, ya kalleta.

  Murmushi tai tace " naga kamar bakasan nace maka Jal sai naga ni sunan naka ne bazan iya fad'a ba to bari na d'au karshe."

  Kallanta yatsaya yanayi zuciyarshi na saka mai abubuwa, harya fara tafiya ya dawo ta window yace" yaushe zaki tafi?"

  Kallansa tai tace " wani abun ne?"

Shiru yai sannan yace " kawai dai tambaya nake."

  Ta lumshe ido tace " bansani ba amma nasan wajen azahar zamu fita da yaya." Tafad'a tana kare ma fuskarshi kallo.

  Baiji dad'i ba yace ok shikenan bye.
  Da sauri tace in na dawo zan iya k'iranka mu had'u a wani gun?
  Kallanta yai sannan ya saki Murmushi yace " za'a barki?"

" nifa in nace inasan abu barina ake inyi."
Zaiyi magana Bala ya dawo tare da cewa malam lafiya? Jalal ya mik'e tare da nuna kata da hannu alamar ta k'irashi yai ciki.

  Sai daya shiga ya tsaya yace " meke damuna? Meyasa bama iya controlling kaina in ina kusa da yarinyar can? Wai yau nine ke tambayar wata......ahhh Jalal yaushe ka zama haka?

   Seemah kam fitowa tai tare da shiga Company d'in kana ganinta kasan tana cikin farin ciki,  tana shiga taga Jalal a tsaye, kallansa tai shima ya kalleta wani sansayar murmushi sukama juna ta wuce shima ya wuce.

    Hmmmmmmmmmm



© *NWA*



��‍♀

1 comment:

  1. Tnx a lot, tnx a million....tnx..tnx...tnx...but then KYAN ALKAWARI CIKAWA...jiya da yau an yi magud'i, d'ad'd'aya aka turo maimakon alkawarin da akai....

    Amma dai mun gode, Allah ya biya...

    ReplyDelete