Sunday, 11 December 2016

JALALUDEEN 2

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
  🐾 *JALALUDEEN*🐾
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾






Na *AYUSHER MOHD*




 No 2⃣




Seemah tana isa gida  a falo ta tarad da Matar babanta tana kwance ta mik'e akan kujera, ta saka apple a gaba tana ci, haushi ya kama Seemah itakam yanda matar takeyi yana bata haushi sam bata santa, ita tanaso taga mutum ya damu da ita bakamar wannan ba.
 Shiga tai tare da tsaya a inda take kwance,  ta kalleta tace "Small mom bakiga na dawo bane?"
   Tad'aure ta d'an kalleta kasa kasa tace " to in kindawo Seemah so kikeyi in mik'e in shiga tsalle? Ga 'yar shugaban kasar England ta iso?"
   Kallaman sun ma Seemah ciwo ta kalleta tace " a gurin iyayena na fi wata sarauniyar England matsayi, amma ina tunanin dole yau injira Dad yazo d'an ya tabbatar miki da hakan."
    Tana kainan ta juya tai d'aki ta fad'a gado, d'an shagwab'a irin na Seemah ta hau kuka baji ba gani, sai data daidaici lokacin dawowar dad ta sake ware murya tana kuka.


   Itakam mata hankalinta ya tashi, gashi batajin zata iya ba Seemah hakuri.

   Dad tare suka dawo su 3 kamar yanda suka fita, haka suke dawowa kullum.
 Dad na shiga ya kalli falon ya saba yana shigowa Seemah zata rugo da gudu ta rungumeshi, ganin ba ta nan yasa ya kalli matarshi yace " Sauda ina Seema?" Cikin rawar murya ta nuna sama, dasauri dad yai hanyar suma su junaid suka bishi.

   Seemah kam jin motsinsu yasa takara sa kuka da sauri suka bud'e kofar, dad ya karasa tare da cewa " Baby menene? Waya tab'amin ke?"
    Seemah Cikin kuka tarik'e hannun dad tace " Dad tambayar ka zanyi, tsakanin ni da sarauniyar England wayafi matsayi a gunka?"

   Da sauri Dad yace " wace irin tambaya ce wannan Seemah? Wake wani zancen sarauniya bayan ni kece sarauniya ta?"
  Ta kalli junaid tace kaifa yaya?
  Ya kalleta yace " Haba princess yama za'ayi ki mana wannan tambayar? Ai ko d'an sarauniyar ne ya nemi yana sanki saboda matsayinki bana jin zamu iya amincemai har sai ya yadda da dokokin mu bare kuma ace matsayi."

   Dariya tai tace " yaya Ammar fa?"
  Dariya yai ya matso tare da rik'e kunnenta kad'an yace " waye ya miki wannan banzar tambayar ke kuma har kika rik'e a ranki?"
Tad'anyi kara tare da kallan Dad tace " Small mom ce."

   A zabure Dad ya mik'e ranshi ya gama b'aci ya juya yai waje da alama gun matar tashi zai je.


    Ammar ya kalleta yace "da baki fad'aba Seemah, Dad bazai mata dasauki ba dama ta b'ata mai rai da safe."
   Seema ta murgud'a baki tace " wayace karta d'inga kula dani? Ni fa yaya banasan mutumin da bai damu dani ba, nafisan kowa na duniyarnan ya soni kar kowa yad'inga nunamin halin ko in kula."

   Dariya Junaid yai yace " lalai Seema ai kuma hakan bazai yiwo ba, tunda mu muna sanki ba shikenan ba? Karki damu dan wani bai damu dake ba."

    Kallanshi tai tadai jishi amma bata aminta ba, itafa tafisan kowa ya sota yakawai......

  Nikam nace tab da matsala........

***********************
Dad kam yana fita ya tarad da Sauda a tsaye a kasan beni, ya kalleta yace " waya baki izinin kid'inga had'amin 'yata da wasu can mutane? Harki samin ita kuka?"

   Tai shiru can tace" Alhaji bafa haka bane kasan me?...."
Katseta yai cikin zafin rai yace " bansan komai ba, kuma banasan insan komai, abu d'aya nakeso in sani, a wani dalilin kike samin 'yata kuka? Ko d'an ke bakisan darajar d'a ba? "

  Cike da mamaki ta kalleshi tace "Alhaji yazaka fad'amin wannan kalmar? Abinfa bai kai nan ba."

  Yace " what?  Bai kai nan ba? In bai kaiba meyasa 'yata na sameta tana kuka? Karki manta zan iya jure komai amma banda hawaye daga idan 'yata, banga d'an Adam d'in dazai wahalarmin da 'ya ba nikuma in kasa d'aukar mataki ba, na aurekine d'an ki kularmin da 'ya kuma akan haka kuka amince daga ke har iyayenki, kukace ku kuma so kuke in barki kiyi karatu a nan kasar na aminta, sannan ni na cika nawa kin gama masters d'inki sai nine bazaki cika min ba?"

    Sauda ta had'iyi wani abu, ta d'aure tace " kayi hakuri, ba da wani abun na fad'aba amma tunda abin ya kai haka amin hakuri."

   Dad baice komai ba ya juya ya hau sama, ta bishi da kallo ranta yakai matuka gun b'aci, tasan sarai me yake nufi da ya hau sama wato ta biyoshi ta bada hakuri.
  Itakam ta rasa wani irin so sukema Seemah, itakam da Seemah gwara a mata kishiyoyi guda 3 su zama su hud'u, in kishiyoyine bata tunanin zasu samu wannan damar, haka ta d'aure tahau sama.

   Seemah na zaune suna hira da shewa sai labarin abin dariya suke bata, itakuma tanayi, can ta d'aure tace "Dad please ka barni inje Nigeria. "

   Dad yace " Seemah mu jira sai wani hutun, ban shirya missing d'inki wannan hutun ba."
   Turo baki tai cikin shagwab'a tace " Dad please ka barni, bafa dad'ewa zanyi ba, sannan ga waya." Tafad'a tana d'aga wayarta.
  Ammar tad'an kalla da alama magana tamai ta ido, shima yace " eh Dad ka barta please ko d'an taje ta gaida su Inna."
  Dad zaiyi magana sallamar Sauda ya katseshi, suka amsa ta karaso ta tsaya a kusa da Seemah, ta saki murmushi tace " Haba Princess daga wasa ashe kinji haushi? Na d'auka tsakanin d'a da mahaifi akwai lokacin wasa?."

  Seemah ta kalleta zatai fitsara Ammar yai saurin toshe mata baki yace " Aunty ba komai ya wuce."
Takalleshi tace " Seemah ina kike san zuwa nazo shigowa naji ana zancen." Tai maganar tana murmushi.

    Seemah tai shiru can tace" gun Yaya Habib nakesan zuwa amma naga Dad kamar bayaso."


Yanda tai maganar ne yasa tabasu dariya, junaid yace " da alama yau zamu ganku a rana Dad."

    Hawayene ya zubo mata tace "dad kaji ko? Gashi ka bari su yaya Junaid zasu mana dariya."

    Da sauri ya jawota ya rungume yace " barshi da gulmarshi, so yake yaga munyi fad'a tunda bai tab'a gani ba, zuwa gun Habib kuwa na amince."
Ihu tasa ta kara rungume dad tace " Dad shiyasa nake bala'in sanka."
  Dariya suka mata Dad yace " Amma in zaki inaji sai na had'aki da securities da zasu d'inga kula dake, haka kawai Habib na can gun aiki ke kuma kina guri ke kad'ai bazan bar hakan ta kasance ba."



   Ta kalli Ammar tad'an lagwab'ar dakai kamar zatai kuka Ammar yace " Dad amma ina ganin kabari kawai in yaso in taje can sai a sanar da Habib ya samarmata bodyguards dazasuna kula da ita. "

  Dad ya kalle Ammar yace "kana ganin hakan ya fi?" Dasauri Seemah tace eh mana Dad.





Nace uhmm..................

****************************

Yau Seemah tun Safe akai wanka dan flight d'in sukai booking, Sauda tafi kowa murnar wannan tafiya d'an ko Seemah dazatai tafiyar ta fita murna.

  Seemah ta shirya cikin riga da wando d'an ita banaji akayanta akwai atamfa ko ince bata tab'a gwada sawa bama, bayan tasa riga da wandon sai kuma ta d'auko rigar sanyi tasa, d'an garin sai da rigar sanyi, ta yi kyau Anna ta kalleta tace " Madam I will miss you."
  Harararta Seemah tai tace " bayan yanzu kin rage damuwa dani?"

  Anna ta karaso ta rungumeta a hankali kwalla ya zubo mata, Seemah ta juyo tace " wasa nake Anna na sani kin damu dani sosai, tun ina karama, nima I will miss u."

     Tare suka fito Anna na rik'e da jakarta, a falo sukaga Sauda sai murmushi take, suna saukowa ta kalli Seemah cikin tsananin farin cikin da kana gani zaka gane tace " Seemah yanzu tafiya zakiyi? Sai kuma yaushe?"

   Seemah ta kalleta ta had'e rai tace " Small mom nasani kinfi kowa murnar tafiya tai, sai dai ba dad'ewa zanyi ba."tana kainan tai waje gun dasu Dad ke jiranta a mota.


Kowa yana zaune a cikin motarsa da driver d'insa, ta kallesu tare da sa dariya tace " Dad ahaka za'ayi rakiyar? Kowa na motarsa? Nima in shiga tawa?"

   Junaid yace " to a ya za'ayi?"

  Ta bud'e motar junaid tace yaya fito, junaid ya fito, ta bud'e motar Ammar tace bros kaima fito, shima ya fito, sukace me za'ayi? Motar Abba ta bud'e ta gaba tace Ya junad shiga nan, ya kalleta yace tohh.
Nan ya shiga ta kalli driver d'in Dad tace fito shima ya fito ta kalli Ammar tace bros jamu.........tafad'a tare da shiga kusa da Dad.


  Dariya sukai nan suka shiga tare da fara tafiya, Dad yace " kai Seema zamuyi missing d'inki, baki tab'ayin tafiya ba tunda aka haifeki."

  Tai raurau da ido tace " yauwa, dole ne kowa a rana ya kirani sau 5 in ba so yake muyi fad'a ba."

   Haka suka cigaba da tafiya ana raha, Dad yace" na fad'ama Habib ya kularmin dake sosai duk abinda kikeso a tabbatar an miki shi."
Dariya tai tace " inada Dad irinka me zai dameni?" Sun isa takira Habib tafad'amai zasu taho.

Sai da aka gama musu checking suka shiga jirgi sannan suka juya zuciyarsu duk ba dad'i.



**************************



Habib na isa company d'insu ya fara shiga meeting,  sun dad'e kafin su gama suka fito sukai sallar azahar, ya duba agoggo akala saura hour d'aya su seemah su iso, yana komawa yataradda wani aikin ya kara tasowa dolene su shiga wani meeting d'in gashi baisan sanda zai fito ba, Secretary d'insa ya kalla yace " Kanwata tana hanya gashi zamu shiga meeting kasa wani ya je airport nan da minti 30 ya jirata ta iso ya tahomin da ita nan, sunanta Seemah, ka tabbatar wanda ka tura mutum ne mai hankali yakuma je ya jirata yanda tana isow zai kawomin ita."

   Secretary d'in ya amsa da to, nan ya shiga tunanin wazai tura, abokinshi ya tuno, dasauri ya danna number,  daga can aka d'aga yace " ya akai Sagir?"

  Sagir yace " Jalal please kataimakamin meeting zamu shiga da Chairman  to kuma kafin mu fito kanwarsa ta iso shine ya keso a taimaka d'aukota, nikuma banyi tunanin kowa a company d'in nan ba sai kai."

  Jalal yai tsaki yace " ta hawo taxi mana? Dole sai an d'aukota? Ni ma aiki nakeyi."

  Sagir yai dariya yace " Taxi jalal? Kanwar Chairman d'in company d'inmu fa nace? Kuma bana tunanin ma ta tab'a zuwa kasar'"


  Jalal ya nisa yace" to kanwar Chairman tafi karfin taxi?"
"Nidai plz kataimakamin abokina d'an Allah, sunnanta Seemah, bari na shiga meeting zan ba da makullin motar chairman d'in akawo maka, nan da 30mins zasu iso."Sagir nakainan ya kashe wayar.

  Tsaki Jalal yai sannan ya kalli takardun da aka bashi yai sorting,  shifa baisan rainin hankali, shi driver ne? Dandai Sagir ne amma da ina..............





By *Ayusher Mohd*
© *NWA*

No comments:

Post a Comment