����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MOHD*
No. 1⃣3⃣
Jalal na fita ya saki murmushi sannan yai hanyar office d'insu, yana shiga yaga duk sun yo kansa da mamaki ya kallesu yace "Lafiya?"
Sukace " me ta maka? Korarka za'ai ko suspension za'a baka?"
Tsaki yai sannan yace " kubani hanya please." Nan suka matsamai ya wuce yana zama wannan macen tazo kusa dashi tace " Sanka take ko?"
Cik'e da mamaki Jalal ya d'ago ya kalleta yace " Sara baki da aiki sai gulma ko? Ke yanzu a tunaninki yarinyarnan ce zata so ni? Kedai sai ki d'inga abu ba tunani."
Matsowa ta kara yi tace " kudai maza wani sa'in u are too slow, ni ai daga yanda naga tanayi nasan sanka take."
Jalal ya had'e rai yace " Get lost"
Matsawa tai tare da tab'e baki tai tace " Zamu gani ai."
Sai dai me? Kalmar ta tsayama Jalal a rai sai nanatawa yakeyi sai dai ya girgiza kai yace " No"
○●○●○●○●○●○●○●○●○●○●
Seemah kam Office d'in Habib ta koma Sagir ta gani tace " har kun gama?" Ya kalleta yanaso yaji me tama Jalal amma yana tsoro, hakan yasa yace " a'a takardu nazo d'auka." Tai gyaran murya tace " Uhmm number abokinka zaka bani."
Eyyye? Sagir ya fad'a cikin tsananin mamaki, juya kai tai tace " kai banasan fassara nemansa nakeyi d'an banaji zan iya kyaleshi yaci mutuncina jiya yanzu kuma naje office d'in baya nan."
Sagir yace " Au hoo na zata......."
Da sauri ta katseshi tace banasan wani shirme, kada ka kuskura ka kawo komai a ranka d'an nafi karfin abinda kake tunani.
Da sauri Sagir ya bata number sannan ya bata hakuri ya juya.
Number ta kalla tad'an rangwab'ar da kai tace "me zan sa? Jal? Mr pride? Jerk? Kind? Ahhh so frustration." Tafad'a tare da tagumi.
Ta kara kurama number ido tace me kakeso insa maka Jalal? Gefe ta kalla kawai taga Jalal ya kashe mata ido yace " *SPECIAL*?
Kai ta girgiza tace noo, tana juyawa taga bayanan kai ta rik'e tace meke faruwa? Jitai anzauna kusa da ita, da sauri ta d'ago jitai Jalal ta gani, ya had'e rai yace " karki kuskura kisamin sunan mutunci kisa *Bad guy* kallansa tai sai taga bayannan, ihu tasa da karfi tare da marin fuskarta tace " I think I am going crazy."
Da sauri ta ajiye wayar a gefe tana girgiza kai, jitai wayarta tayi kara ido ta runtse sannan ta d'au wayar Ammar ne hakan yasa tai ajiyar zuciya ta d'aga, Ammar yace " Swthrt Dad yace strike yakeyi tunda wai ke bakya nemanshi kullum shi yake k'iranki."
Shiru tai Ammar yace Seemah? Tace " yaya da alama bani da lafiya," yace meya sameki? Ajiyar zuciya tai tace " Bakomai ina Dad d'ina?" Ammar yace ya fita ki kirashi."
Tanaji haka ta katse wayar tare da kallan number Jalal da sauri tasa " No name."
Ta ajiye wayar tare da shigewa cikin cinyoyinta, sai dai me? Jalal ta hango sanda ta kusa fad'uwa ya tarota, bud'e idanta tai da sauri tare da d'aukan waya ta k'irashi.
Jalal na zaune yaga new number, hakan yasa yad'aga tare da sallama a sanyaye, Seemah najin muryarsa ta kasa magana Jalal nata hello? Hello? Hello? Jin shiru yasa ya katse, kallam wayar tai tace lafiyata kalau fa na fito daga gida, d'an haka dolene in k'irashi inji meyamin nazama haka.
Kara k'iranshi tai nan ma takasa magana ya k'ara kashewa tare da sakin tsaki yace network ne ko iskancin mutane?.
Yana ajiye wayar aka sake k'ira sai data kusa katsewa ya d'aga tare da fita daga office d'in yace " wai meye hakan? In baza'ai magana ba meye dalilin k'iran?" Har zai katse yaji ance " wato kai haka Allah yayika baka da hakuri ko?" Cike da mamaki yace "Seemah?" Murmushi tai tace " Suprise!!!" Da mamaki yace a ina kika sami number ta?
Tab'e baki tai tace " Agun Sagir na ansa saboda in ina nemane kaini wani gurin karnasha wahala." Cike da masifa yace " What? Inkina neman me?"
Katse wayar tai sannan tace " bana cikin hankali na, me zanyi da mutum irin wannan?" Jitai ance Seemah me kike a kasa?
Da sauri ta kalli Habib tace yaya ka dawo? Tafad'a tare da mik'e wa.
Yace" na dawo, zaki gida ne?" Tace eh yace ok bari na k'ira driver d'in.....
Jalal kam wayar yabi da kallo yace " meke nan? Wai ni meyasa yarinyar nan ta gama rainani? Shine har waccen zatace me? So? Yarinya ta gama rainan hankali lalai ina bukatar seta ta."
Yama kainan ya juya ciki.....
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Sun fito itada Habib ya kalleta yace " Seemah badai abinda ya faro a Suleja bane yake damunki?" Kallansa tai tare da sakin murmushi tace " basu da laifi yaya, ace ina jikarsu amma ko sau d'aya ko a waya ban tab'a k'iransu bafa shekara 20 kenan fa."
Habib yai shiru shidai har ga Allah bai yadda wai rashin zuwantane yasasu haka ba, tabbas akwai wani abu zai k'ira Dad......
Seemah ce ta katseshi da cewa "Yaya karfa kafad'ama Dad kasan yamda yake ji dani bazaiji dad'i ba." Ya kalleta yace to seemah.
Ta shiga mota, suka fara tafiya wak'ar Kabhi Kushi Khabi Gam ke tashi a motar, haka kawai tasamu kanta da lumshe ido tare da jingina kanta saman kujerar motar wak'ar har cikin jikinta take jinta.
Har suka isa gida bama tasan sun iso ba sai da Bala driver ya fad'a mata sun iso, sannan ta kalleshi tace cassette ne? Yace eh tace ciromin, nan ya ciro mata ta amsa tai ciki.
Tana na shiga gida taleka falo taga Farida na zaune a gaban laptop da alama aiki take, Sannu da gida kawai tace mata ta wuce d'aki, Aisha batanan da alama tana skul hakan yasa Seemah ta fad'a gado tai ajiyar zuciya ........
© *NWA*
��♀
No comments:
Post a Comment