Thursday, 15 December 2016

JALALUDEEN 14

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MOHD*


   No. 1⃣4⃣

   Juyi ta shiga yi akan gado, hartazo bakin gado bata sani ba tana juyawa kuwa ta murgino jikake tummm, zafin fad'owar datai yasa ta saki kuka, Farida na jinta a ranta tace " wannan shagwab'a tayi yawa wlh." Aikinta ta cigaba dayi.

  Seemah kam kuka tai tayi ta d'ade kafin ta daina ganin ba mai lallashinta waya ta d'auka tace inkirashi? Kai rainani zaiyi, saurin kiran Junaid tayi yana d'agawa cikin shagwab'a tace " yaya fad'owa nai daga kan gado." Dariya yasa yace " tunanin me kanwara take har ta fad'o bata sani ba? Ko barci kike?"
   Ta turo baki tace " ni kaina bansan tunanin danakeyi ba yaya."
   Cikin zolaya yace " ba dai tunanin soyayya takeyi ba ko?"
   Da saurin tace " haba yaya ni d'in? Bafa san sa nake ba wlh."
  " dagaske kenan akwai wanda kike so?" Ya fad'a yana jiran amsarta.
  Tace " wlh yaya a'a kawau bansan meke damuna bane jiya da yau."
  Yace " uhmmm kanwata u look suspicious, da alama akwai wani abu a kasa."

  Saurin katse labarin tai da cewa yaya ina wannan budurwar ta ka?
  yace" Seemah kedai bari ta rainamin hankali ashe bani takeso ba kud'ina takeso, kai mata akwai matsala."
  Cike da mamaki Seemah tace " yanzu yaya duk yanda take nuna maka da kulawar datake baka dama ta karya ce?"
  Yace " u have to be carful."

Dariya tai tace " ai ni yaya wanda zan aura sai ya bani jinin jikinsa saboda tsabar soyayya sannan sai ya amince akan duk abinda nakeso."

  " tab lalai zanso ganin wannan saurayin, da alama Ammar ne zai nemo miki saurayi mai halayyarsa d'an inba wanda yake sanki kamar shi ba banajin zaki samu abinda kikeso."
  Turo baki tai tace " Dama ai nasan duk cikinku Ya Ammar yafi sona gashinan ka fad'a da kanka."

  Dariya yasa yace " Seemah tun kina karama baki ga yanda yake ji dake ba, sanda kina yarinyafa indai kika zazzabi to shima sai yayi. "

  Murmushi tai tace " nima ai shiyasa duk nafi sanshi."

Sun dad'e suna hira kafin suyi sallama, Seemah tabi wayar da kallo number Jalal ta bud'e tace in k'ira? Wata zuciyar tace ki k'ira kice me? Wata kuma tace ki k'ira ko muryarsa kyaji.

  Dialing ta d'anna har ya kusa shiga ta kashe da sauri sannan ta bud'e gub text, ta rubuta " me kake yi?" Tana gamawa ta goge ta sake rubuta " Kana office?" Nan ma ta goge ido ta rufe tace " what should I do?" Kara d'aga wayar tai tasa " kana ina?"
Bata sani ba hannunta yai sending ihu tasa tara da danne kanta da pillow tace ya zanyi, me zai ce.

   Jalal ya fito zaije masallaci yaji text ya shigo da mamaki ya kalli number sannan ya bud'e text d'in, tambayar ta d'aure mai kai dialing d'in number yai

Seemah najin ringing takalli wayar sai datai ta ajiyar zuciya tare da furzar da iska tana cewa Cool Down kafin ta d'aga wayar,  Jalal da mamaki yace " Waye? Kuma bangane tambayar inda ta dosa ba."

  Cikin takaici Seemah ma tace " waye ban gane maganar da kake yi ba, kasan number daka k'ira dai ko."

  Jalal yai murmushi yace " Au kece?"
Tace " nice sai me? Karkuma kai tunanin na tambayeka ne saboda wani abun ko na damu naji kana ina, na tambayeka ne d'an ina wani guri so nake ka maidani gida."

   Kai ya girgiza sannan yai murmushi yace " da alama dai damuwar ki kai dani, tunda a tunanina dai ban tambayeki ba."

  Mik'ewa tai tsaye tace " inji wa? Ni na damu dakai? Ha ha ha, ko a mafarkina."

  Murmushi kawai yakeyi tana gamawa wata dabara ce ta fad'omai yace " au to shikenan dama na d'auka kin damu danine yasa kika k'ira har zanyi tunanin k'iranki nima akai akai amma tunda ba haka bane shikenan."

  Da sauri tace " a'a ba cewa nai bandamu dakai ba gaba d'aya amma da gaske ne zaka d'inga k'irana?"

" zancen k'ira kuma ai ya roshe tunda ba damuwa kikai dani ba, sai anjima." Yana kai nan ya katse layim tare da sakin wani sansanyan murmushi yace " yarinta ke d'ibanta ko gatane ya mata yawa?"



  Seemah kam wayar tabi da kallo tare da fad'awa gado rigim kamar wacce ta suma a hankali tace " shikenan na bada kaina, dama ya rainani gashi na kara bada wata kofar." Sai kuma tai shiru can ta mik'e zaune tare da d'aura pillow akan cinyarta tace amma shima menene namin wannan tambayar?

Juyawa tai kawai taga Jalal a tsaye ya juya baya sai kuma ya juyo cikin salon soyayya yace " saboda naga kin damu dani."
Kwanciya takara yi ta rufe kanta cikin bargo tana cewa No! No! No!...........

  Jitai an yaye bargon kad'an Aunty farida ta gani kallanta tai kamar me bacci tace " ya akai Aunty?" Farida tace " Bake bace dama? Inatajin ana kamar magana ne nama d'auka kece."

  Jan bargon ta sakeyi tace bani bace.
Farida ta fita tana mamaki to daga inane?




© *NWA*

��‍♀

7 comments:

  1. This comment has been removed by the author.

    ReplyDelete
  2. Waiting is one of the most energy sapping, emotional draining, psyche destabilizing, brain stressing, heart jolting and psychogically traumatizing action or rather inaction most especially for hyperactive people like him...BUT MUNA DAI JIRA.

    ReplyDelete
  3. Thanks for the support, hope kunajin dad'in littafin?

    ReplyDelete
  4. Gaskiya in dai opinion dina za a yi amfani dashi kuma kan wannan littafin jalaluddeen toh wallahi za a ba ki/ka Literature Nobel prize. Saboda na Dade rabona da zama engrossed a kan littafin Hausa Duk da na kan karanta prologue ko preview Amma sam ba sa burgeni Balle na ci Gabas, amma tun ranar da na fada karanta shi na kasa fitar dashi daga raina, nayi wa mutane sun fi ishirin magana su nema min complete book, ina jin mutane sun kai hudu ko Biyar sun miki magana daga wajena, har beely badaru na nema da SK baby mash da Nbaba Mada da sauransu don su Roka min complete book din from you. Kuma ina jin har nambarki/ka na yi adding a whatsapp kuma mun yi magana Duk don littafin. Hakanan a Facebook which you are yet to respond, all this before na samu blog dinki/ka, kuma before u even start posting here, I was checking everyday. Well Alhamdulillah, finally we are here, sai dai za a sha wahalan jira. But if please help and be posting at least 3 episodes.
    Allah ya kara basira, ya kuma amfanar, Allah ya kyautata niyya saboda kurakuran ciki na gangar ko na kuskure su zam abun gafartawa, kuma nasihar ciki da irshadi da nishadantarwa da ilmantarwa su zama gurbi a littafin lada.
    Thanks and keep up.

    ReplyDelete
  5. Nagode sosai, insha Allah zan dinga posting 2 pages a rana amma 3 pages yayi yawa.....lol

    Tnx 4 d support.

    ReplyDelete
    Replies
    1. To Allah ya saka da alkheiri, gaskiya an tausaya kuma an taimaka, Allah ya kara daukaka, basira, juriya ya kuma biya bukatu.
      The book has taken a new suspensive dimension and somehow striking a resemblance with a life of a real person I know, Amma mu je zuwa da.

      Delete