����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MUHD*
No. 1⃣6⃣
Jalal na shiga office ya shiga duba takardun d'azu wayar Zainab ce ta shigo hakan yasa ya tuna kalaman Seemah na in da gaske ne yabari ta katse sai ya k'ira, yana kallan wayar harta katse sannan ya k'irata yana d'agawa tace " Yaya ya zakayi?"
Cike da mamaki yace name fa?
Tace " dazu su baffana sukabar gidan nan dashi da Abba wai sun yanke auran mu zasuyi."
Jalal cikin b'acin rai ya mik'e yace " me?"
Zainab hawaye ya zubo mata tana tsananin san Jalal hakan yasa batasan wani abinda zai b'atamai rai ciki kuwa harda auranta gani take in bayaso to fa zata iya hakura sai dai batajin zata auri wani.....
Jalal ne ya katseta da cewa nagode kanwata bari na k'ira Abban, kana katsewa yak'ira Abba tare da fita daga office d'in, Bayan sun gaisa Jalal yace " Abba yanzu Zainab ta........"
Cikin fishi Abba yace " kai ko kunya bakaji ba Jalal? Yarinyar nan tun tana shekara 12 mahaifinta ya baka ita sannan alokacin ta dawo gidanmu take taya mahaifiyarka kula da kanwarka da kuma aiyukan gida, har kawo iyanzu, sannan duk sanda na maka maganar auranta sai ka wayance da wani abun, gashi ta girma mahaifanta nasan suga tayi aure, shine ko kunya dan munyi zancen auranku zaka k'irani ka nemi yin korafi?"
Jikin Jalal yai sanyi ya sani sarai Zainab nada hankali gashi tun tana karama take musu wahala, sai dai shifa bai tab'a jin santa ba banda na 'yan uwantaka, cikin sanyin murya yace " Abba ba haka nake nufi ba."
Abba yace " karka kuskura ka b'atamin rai, kai ba wata kakeso ba yanzu shekarunka 28 to me kake jira? So kake sai ka tsufa ko me?"
Jalal yai shiru dakyar yad'aure yace " Abba yahakuri."
Abba yai shiru can yace " Jalal karka manta ba komai garemu ba, da abinda zamuci a rana ma wahala yake mana cikin wannan tsananin kai karatunka har ka samu aiki, kaine gatanmu damu da kanwarka banaso zuciya tad'inga saka maka abinda bazai amfane ka ba."
Jalal yace " nasani Abba."
Abba najin haka ya katse layin dan zuciyarsa tafara raunana, yana katsewa ya kalli Umma dake zaune idanunta taf da kwalla tace " Alhaji kad'inga mai a hankali kasan wahalhalun dayasha a da, ni nasani Jalal mai biyayya bazai bijire maka akan auren Zainab ba."
Abba ya kalleta shima cikin tausayi yace "Har yau bana manta wahalar da yaron nan yasha, ga makaranta secondary ga aikin karfi dayake yi na tara kud'in makarantar dazai shiga jami'a da ita, ga rashin abinda zamuyi amfani dashi a gida, haka zai fasa asusunshi ya bani kud'in,a ciki za'ai amfani da na gida dana magani Zaheeda," ajiyar zuciya yai yace " Ni kuwa ina zan manta hajiya? Kawai ina tsoro ne, kar d'an yaje birni wata 'yar masu kud'in ta nemi jan ra'ayinsa."
Umma ta share hawayen dake gudu a fuskarta tace " Ai *Jalaludeen* namijin duniya ne, tun yana karami yake kula damu hakan kuma banaji yanda yake da dakkakiyar zuciya akwai yarinyar da zata nemi juyamai tunani."
Shiru sukai a hankali idan Umma yakai kan Zaheeda dake kwance idanunta a rufe suke amma hawaye da zubowa ta gefen idanunta kura mata ido tai a ranta tace Allah yabaki Lafiya....nace Amin.
Jalal suna gama waya da Abba yatsaya agun yai shiru kara text ne ka tseshi daga tunanin da yake, wayar ya d'aga ya karanta sakon, " Ka gama?"
Ido ya runtse sai kuma wata zuciyar tace " menene na damuwa? San Seemah kake?" Da sauri yace a'a mezanyi da wannan karamar yarinyar da shagwab'a da yarinta suka mata yawa, iska ya furzar sannan ya koma office ya d'auko takardu yai kasa, sqi daya gama sannan ya mata text akan ta sauko su tafi.
Seemah kam takaice ya ishe ta kamar ita? Ace tayi hour 1 tana jiran d'a namiji ina....da sake, sai dai ya zatai tunda ta kori Bala, haka ta sauko fuska a d'aure, a kusa da motarta ta ganshi batace mai komai ba ta mik'amai key ya shiga itama ta zagaya tashiga ya ja mota suka fara tafiya, sunyi nisa ba wanda yama wani magana shi abinda ke damunshi daban itakuma takaicinta ko hakuri ma bai bata ba, cikin b'acin rai tace " Yanzu da gaske baka da niyyar bani hakuri?"
Kallanra yad'anyi sannan yamaida fuskarsa kan titi yace da nai me fa?
Takalleshi tace " mene? Ka barni a waje sama da hour 1 kace me? Dakai me?"
Jalal ya karasa gefen titi yai parking sannan ya juyo cikin b'acin ran abinda ake shirin yimasa yace " me? Na barki na hour 1? Ko kin manta aiki nake kika sani na fito? Ido ya rufe sannan ya ware hanayyensa ya nunata dasu yace " Seemah I am not in a good mood d'an haka kibini a hankali karki b'atamin rai."
Seemah yanda yake mata fad'a yasa ta tsorata tunowa tai d'azun nan fa suka gama hira da murmushi yanzu kuma menene hakan? Tad'auka zai bata hakuri komai ya wuce, cikin halin ko in kula tace " amma nikam kai wani irin mutum ne?"
Jalal ya juyo ya maka mata wani mugun kallo sannan ya fizgi motar a guje, ganin yanda yake gudu ta had'iyi yawo tace " amma ko me aka maka nina maka?mutum sai kace mai aljanu?"
Shidai Jalal bai kulata ba gudu kawai yake yana zuwa kofar gidansu kafin a bud'e yai kashe motar ya fito daga motar dakarfi ya rufo motar yai gaba, Seemah ta bishi da kallo baki bud'e tace " Ha ha Ha me kenan?"
Cikin takaici itama ta fito daga motar a kofa tacema Bala ya shigo da motar tai ciki.
Tana shiga tai d'aki ta fad'a gado batama kula Aisha na zaune ta baza tagumi ba, Aunty Farida ce ta shigo tace " Seemah kin dawo?" A hankali tace eh.
Farida ta karasa gun Aisha tace " wai ke wace irin soyayya kike yi hakan? Ba tunani ba kuma tsari?"
Aisha ta d'ago idanunta tace " Aunty yazanyi da san Muftahu?"
Farida tace " Shiyasa yake miki abinda yaga dama tunda ya kula ke kika damu dashi, yaushe rabon ya k'iraki? Sai ke kece uwar soyayya ko? To wlh indai haka zaki cigaba gaba ko a titi yaganki d'auke kai zaiyi yai kamar be ganki ba."
Seemah tayi shiru tana jinsu itama da alama ita take neman Jalal duk da ba soyayya suke ba amma ta kula shike jawo mata raini.
Farida tacigaba " kinsan me akecema *Hard to Get?*"
Kad'a kai tai alamar a'a
Ta cigaba bani wayarki nan ta mik'a mata Farida tace yasan duka layinki biyu? Tace a'a da Mtn kawai muke waya kinsan bana waya da Airtel sosai, Farida ta bud'e wayar tare da cire sim d'in Mtn d'in tace daga yau karki kuskura ki kara kiransa, duk san ki k'irashi dazakiji kar ki nemeshi, shikuma rashin ganin kiranki da farko zaiji dad'in kin kyaleshi amma ahankali abinzai fara damunsa, wannan shi ake kira Hard to get.
Seemah ma ta mik'e tana kallan Farida tace " kai Aunty kice shiyasa kika rikitamin yaya.
Dariya tai tace "Allah Aishan ce haushi take bani kuma wlh ki kuskura ki kirashi inji."tanakainan tafita.
Seemah ma tace nima dole inyi hakan.
© *NWA*
��♀
Kudos.
ReplyDelete